in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sahara na tsakanin yanayi mai dausayi da kanfon ruwan sama a kowane shekaru 20,000
2019-01-04 20:19:41 cri

Wani nazarin bincike da aka wallafa a mujallar ci gaban kimiyya ranar Laraba, ya nuna cewa, a cikin kowane shekaru 20,000 hamadar Sahara da yankin arewacin Afirka suna tsakanin yanayi mai dausayi da kuma kanfon ruwan sama.

Masu buncike daga cibiyar nazarin fasahar kere-kere ta Massachusettes (MIT) sun bayyana cewa, canjin yanayin yana faruwa ne sakamakon yadda rana ke kewaya duniya, wadda hakan kan shafi yawan hasken rana da ake samu a lokuta daban-daban.

A cewar farfesa David McGee, na sashen nazarin kimiyyar duniya na cibiyar ta MIT, suna ganin wannan lokaci ne mai muhimmanci da za su gano tarihin hamadar Sahara da lokacin da ya fi dacewa dan-Adam ya zauna a hamadar ta Sahara da kewayenta har ma fiye da nahiyar ta Afirka, da kuma lokatun da ba su dace da rayuwar dan-Adam ba kamar yadda ake ciki a yau.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China