in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pompeo: Shirin Iran na harba roka sararin samaniya ya saba kudurin MDD
2019-01-04 19:25:29 cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, shirin da kasar Iran take yi na harba makamin roka sararin samaniya ya saba kudurin kwamitin sulhu na MDD, inda ya bukaci kasar ta Iran da ta dakatar da ayyukan da abin da ya shafa.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta fitar, Pompeo ya yi gargadin cewa, shirin da Iran take yi na harba na'urori guda uku a cikin watanni masu zuwa zai nuna a fili yadda kasar ta yi fatali da kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2231.

A wannan rana ce kuma, ministan harkokin wajen kasar ta Iran Mohammed Javad Zarif ya yi watsi da gargadin na Pompeo, yana mai cewa, harba rokoki da gwajin makamai masu linzami na kasarsa ba su saba kudurin ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China