in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta bukaci a samar da dawwamamman zaman lafiya a Sudan ta kudu
2018-12-15 15:53:57 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR a jiya Juma'a ta bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Sudan ta kudu dasu tabbatar da daukar matakan wanzar da zaman lafiya don kawo karshen gararambar da 'yan kasar ke yi a sanadiyyar yakin basasar shekaru 5 da kasar ta fada cikin sa.

Filippo Grandi, babban jami'in hukumar 'yan gudun hijirar MDDr ya jaddada kiransa ga dukkan bangarorin dake rikici da juna da su ci gaba da daukar kwararan matakan da za su taimaka wajen samar da dawwamamman zaman lafiya don kawo karshen tashin hankalin da ya barke a kasar.

"Mutanen Sudan ta kudu, mafi yawancinsu suna warwatse ne a sansanonin 'yan gudun hijira inda suka shafe tsawon lokaci a wannan yanayi, ya dace a kawo karshen halin kuncin rayuwa da suke fuskanta," in ji Grandi, ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake tunawa da cika shekaru 5 da barkewar yakin basasar Sudan ta kudun.

"Dole ne a tabbatar da zaman lafiya. Mummunar illar da tashin hankalin ya haifar za'a dauki tsawon lokaci kafin komai ya daidaita, amma za'a iya cimma wannan nasara ne kadai idan bangarorin da ba sa ga maciji da juna suka amince da shiga tattaunawar zaman lafiya, da lalibo bakin zaren warware rikicin ta hanyar siyasa, kuma su amince da ajiye makamansu har abada," in ji jami'in.

Jaririyar kasar ta kasance a matsayin yanki mai fama da rashin zaman lafiya, rikicin kasar ya raba kusan mutane miliyan 4 da muhallansu, inda suke neman mafaka a ciki da wajen kasar, in ji MDD.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China