in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar SPLM-IO ta Sudan ta kudu za ta shiga yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe
2018-08-29 09:55:30 cri

Babbar kungiyar adawar Sudan ta kudu SPLM-IO ta amince za ta sanya hannu kan yarjejeniyar karshe ta tabbatar da zaman lafiya a kasar, bayan a lokutan baya ta yi biris da amincewar, ma'aikatar harkokin wajen Sudan ce ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa.

Tattaunawar zaman lafiyar Sudan ta kudu ta baya bayan nan da aka gudanar, an kammala ta ne a ranar Talata a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, inda shugabannin gwamnatin Sudan ta kudu da jam'iyyun siyasar kasar suka rattaba hannu kan yarjejeniya ta karshe don kawo karshen tashin hankalin da ya ta'azzara kasar.

To sai dai kuma, babbar kungiyar adawar kasar ta (SPLM-IO) wadda Riek Machar ke jagoranta, ta ki amincewa ta sanya hannu kan yarjejeniyar.

Sanarwar da ministan harkokin wajen Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed ya fitar ta bayyana cewa, gwamnatin Sudan ta fara gudanar da wata cikakkiyar tattaunawa tare da madugun 'yan adawar kasar kuma shugaban kungiyar 'yan tawayen ta SPLM-IO, Riek Machar, inda daga bisa Machar din ya amince zai sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a gobe ranar 30 ga watan Agusta.

Ministan ya yi alkawarin zai gabatar da wasu batutuwa da Machar ya bukaci a yi la'akari da su a lokacin taron kolin kungiyar hada kan kasashen gabashin Afrika IGAD, inda kuma ya bukaci a tattauna kan batutuwan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China