in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da aikin dawo da jirgin saman kasar
2018-09-20 09:37:13 cri
Karamin ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ya ce gwamnatin Najetiya ta dakatar da aikin dawo da jirgin saman kasar da ta yi ta yayatawa.

Ministan ya bayyana cewa, an yanke shawarar ce, yayin zaman majalisar zartarwar kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya Laraba, Amma kuma bai yi wani karin haske game da dalilan dakatar da aikin dawo da jirgin saman kasar mai suna "Nigeria Air" ba.

Ministan ya shaidawa manema labarai a Abujar, fadar mulkin kasar cewa, matakin ba shi da nasaba da matsin lamba daga masu ruwa da tsaki ko wani dalili na siyasa.

Tun farko dai gwamnatin Najeriyar ta yanke shawarar dawo da jirgin saman kasar ne, saboda rashin karfin jirgin da ake da shi a halin yanzu na biyan bukatun 'yan kasar.

Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Yulin wannan shekara ce, Najeriya ta kaddamar da suna da tambarin jirgin, yayin wani bikin baje kolin jiragen sama a birnin London. A watan Disamban wannan shekarar ce dai aka shirya jirgin zai fara aiki da jarin dala miliyan 300. An kuma tsara cewa, sassa masu zaman kansu ne za su tafiyar da harkokinsa, a yayin da gwamnatin Najeriya za ta mallaki kaso 10 cikin 100 kacal na jarin kamfanin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China