in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta taya Sin murnar nasarar saukar na'urar binicke ta Chang'e-4 a duniyar wata
2019-01-05 15:20:48 cri

Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya taya kasar Sin murnar samun nasarar saukar na'urar binicke ta Chang'e-4 wadda kasar Sin ta harba duniyar wata.

Shugaban kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Juma'ar da ta gabata a lokacin da yake ganawa da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar mista Wang Yi a helkwatar kungiyar AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

"Ga bil adama, bangaren wata wani waje ne da ya fi karfi zuwa, amma sakamakon irin karfin manyan fasahohin da take da shi, kasar Sin ta samu nasarar harba na'urar binciken wadda a yanzu haka ta sauka lami lafiya, wannan babban abin tarihi ne," in ji jami'in na AU.

Ya nanata cewa, Afrika, babbar aminiya ce ga kasar Sin, tana matukar farin ciki da irin nasarorin da kasar Sin ta riga ta samu, Faki ya bayyana kyakkyawar fatarsa cewa, kasashen Afrika za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin kimiyya da fasahar kirkire kirkire.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China