in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Sin a fannin ababan more rayuwa
2017-07-03 08:51:06 cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta bayyana kudurinta na kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannin samar da muhimman ababan more rayuwar jama'a, duba da yadda kasar ta Sin ke kara zuba jari a wannan fanni.

Kwamishinar kungiyar AU mai kula da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da makamashi Abou-Zeid Amani ce ta bayyana hakan ga taron manema labarai yayin taron kolin kungiyar karo na 29 dake gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ta ce, ta yi na'am da dinbin jarin da kasar Sin ta ke zubawa a bangaren muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da harkokin watsa labarai da sadarwa na zamani (ICT) da kuma makamashi.

Jami'ar ta kuma bayyana cewa, akwai tarin damammaki da nahiyar za ta ci gajiya daga shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar, da kuma ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.

Ta ce, kungiyar AU tana fatan kara zurfafa hadin gwiwa da Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China