in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin: Kamata ya yi MDD ta hada kai da AU domin warware matsalar Afirka
2017-09-13 11:25:27 cri

Mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haotao ya bayyana cewa, kamata ya yi MDD ta kara hada kai da AU domin dakile kalubalen da kasashen Afirka ke fuskanta.

Wu Haitao wanda ya bayyana hakan a yayin bainar jama'a da aka gudanar kan huldar abokantaka dake tsakanin MDD da AU, ya bayyana cewa, yana da muhimmanci a kara nuna goyon baya ga ci gaban kasashen Afirka, a don haka ya kamata MDD da AU su kara hada kai don samun nasarar aiwatar da ajandar MDD game da samun dauwamamman ci gaba nan da shekarar 2020 da ajandar AU game da raya Afirka nan da shekarar 2063 yadda ya kamata, musamman ma wajen samar da tallafin kiwon lafiya da ba da ilmi da tattalin arziki da cinikayya da samar da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a.

Kana ya kara da cewa, kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka domin cimma burin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a nahiyar ta Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China