in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta zurfafa hadin gwiwa da AU a fannoni biyar
2017-06-22 09:37:44 cri

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na zurfafa hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Afirka (AU) a muhimman fannoni guda biyar.

Da yake karin haske game da wadannan fannoni da sassan biyu za su zurafafa hadin gwiwa a tsakaninsu, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat a hedkwatar kungiyar ta AU da ke birnin Addis Ababan kasar Habasha, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce fanni na farko shi ne daidaita dabarun bunkasa sassan biyu, ta hanyar mayar da hankali wajen yayata tare da aiwatar da muhimman sakamakon da aka cimma a taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu.

Fanni na biyu a cewar ministan na Sin, shi ne zaman lafiya da tsaro, duba da irin taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka, ta yadda za su bunkasa karfinsu na tabbatar da tsaro da zaman lafiya, da kuma yadda za su warware matsalolinsu da kansu.

Fanni na uku, shi ne karfafa hadin gwiwar kiwon lafiyar jama'a. Kasar Sin na fatan taimakawa bangaren kiwon lafiyar nahiyar ta Afirka, ta hanyar gina cibiyoyin kare yaduwar cututtuka(CDCs) a kasashe Afirka. Kana bangaren na hudu shi ne kudurin da kasar Sin ke da shi ne na taimaka wa kasashen Afirka samun kwararru ma'aikata ta hanyar samar musu da horo.

Bangare na biyar, kana na karshe da sassan biyu ke fatan zurfafa hadin gwiwa, shi ne mayar da hankali kan daidaita batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya ta hanyar kare 'yanci da muradun kasashen Sin da da Afirka, har ma da na kasashe masu tasowa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China