in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron kasuwanci karon farko tsakanin Sin da Afrika a Habasha
2018-12-04 09:52:11 cri

An kaddamar da taron kasuwanci karo na farko, tsakanin kasar Sin da Afrika, jiya Litinin a birnin Addis Ababa, a daidai lokacin da 'yan kasuwar Habasha da na kasar Sin ke da burin hada gwiwa a bangarori da dama.

Yayin taron kasuwancin tsakanin Sin da Afrika, dake gudana daga jiya 3 ga wata zuwa gobe 5 ga wata, mai taken "baje kolin ayyukan masana'antu na hadin gwiwar Sin da Habasha", za a gudanar da wasu shirye-shirye, wadanda suka hada da taron manyan jami'ai kan kasuwanci da taron inganta zuba jari da na hadin gwiwa kan ayyukan masana'antu da kuma ziyartar yankunan masana'antu na kasar Habasha.

Yanzu kamfanoni kasar Sin 46 ne ke baje kolin hidimomi da kayayyakinsu a zagaye na farko na taron.

A jawabinsa yayin bude taron, Melaku Ezezew, shugaban cibiyar ciniki da kungiyoyi kasuwanci ta kasar, ya jadadda alakar kasuwanci mai karfi dake tsakanin Habasha da kasar Sin, a matakan gwamnati da kasuwanci, inda ya bayyana cewa, taron zai taimakawa kamfanonin karfafa hadin gwiwarsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China