in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin Sin ya samar da guraben aikin yi ga al'ummar Habasha
2018-11-24 16:38:46 cri

Karamin ministan harkokin wajen Habasha Aklilu Hailemicheal, ya ce jarin da kasar Sin ta zuba a kasarsa cikin shekaru 20 da suka gabata, ya samar da guraben aikin yi ga al'ummar kasar da dama.

Ministan ya bayyana haka ne a wani taron karawa juna sani da ya gudana tsakanin lardin Zhejiang na kasar Sin da Habasha, kan harkokin cinikayya da zuba jari, wanda ma'aikatar harkokin wajen Habasha da hukumar bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kwamitin lardin Zhejiang na kasar Sin suka shirya a birnin Addis Ababa.

A cewar Aklilu Hailemicheal, gwamnati da kamfanonin kasar Sin sun zuba jari sosai a Habasha cikin shekaru 20 da suka gabata, al'amarin da ya kai ga samar da aikin yi ga 'yan kasar masu tarin yawa.

Ya ce, kasarsa na sa ran samun karin damarmaki karkashin shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta kaddamar, wadda ta mayar da hankali ga hadin gwiwa kan harkokin tattalin arziki tsakanin kasashe.

Har ila yau, ya ce jari da dangantaka dake kara habaka tsakanin kasashen biyu da ya bayyana a matsayin 'yan uwa, wani bangare ne na muhimmiyar huldar dake tsakaninsu, wadda ta shafi bangarori da dama, ciki har da cinikayya da al'adu da ilimi da kuma neman ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China