in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nijar sun hallaka mayakan Boko Haram 287
2019-01-03 20:15:11 cri

Jiya Laraba ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta fitar da wata sanarwa, inda aka bayyana cewa, kwanan baya sojojin kasar sun kaddamar da hari a yankin tafkin Chadi dake kudu maso gabashin kasar, inda sun harbe mayakan kungiyar Boko Haram da yawansu ya kai 287 har lahira.

Sanarwar ta ce, tun daga ranar 28 ga watan Disamban shekarar 2018 zuwa 2 ga wannan wata, sojojin sama da na kasa na kasar Najir sun kaddamar da hare-hare inda suka hallaka mayakan Boko Haram guda 287, tare kuma da karbe makamai da dama daga wajensu, kawo yanzu babu sojojin Nijar da suka rasa rayuka ko jikkata

A cikin sanarwar, rundunar sojojin Nijar ta nuna gamsuwa kan sakamakon da ta samu, kuma ta bayyana cewa, matakan da sojojin kasar suka dauka sun gurgunta kungiyar ta Boko Haram sosai.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China