in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi maci domin nuna goyon baya ga mutane Diffa dake fama da hare haren Boko Haram a Nijar
2016-06-06 10:17:49 cri

A ranar Asabar a birnin Yamai na Nijar, daruruwan mutane suka halarci wata zanga zangar lumana domin kawo goyon baya ga al'ummar jihar Diffa dake kuriyar kudu maso gabashin kasar, kusa da Najeriya da kuma sojoji da jami'an tsaron Nijar na FDS dake fama da munanan hare haren kungiyar Boko Haram, a cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake wurin.

Shugabannin kungiyoyin fararen hula, jam'iyyun siyasa da kuma kungiyoyin kwadago, sun halarci wannan maci bisa ihun cewa, "Muna bukatar zaman lafiya", "Mu 'yan Diffa ne", haka kuma sun kira ga gwamnatin Nijar da ta dauki nauyin dake wuyanta yadda ya kamata kan shirin kare al'umma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China