in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar na bukatar agajin gaggawa ga 'yan gudun hijira sakamakon harin Boko Haram dubu 280
2016-06-16 10:05:13 cri

Gwamnatin Nijar ta bukaci gamayyar kasa da kasa da su hamzartar ba da taimakon gaggawa ga mutane fiye da dubu 280 da hare haren Boko Haram suka tilastawa barin muhallinsu.

A halin yanzu, fiye da 'yan gudun hijira dubu 280, kimanin iyalai dubu 40, suke bukatar tallafi a jihar Diffa, dake gabashin Nijar, a cewar cibiyar kula da harkokin jin kai dake fadar faraministan Nijar.

Game da bukatun abinci, mutane dubu 135 da 400 matsalar ta shafa, bisa darajar kudin da aka kiyasta zuwa fiye da Sefa biliyan 3,2 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 5.3.

Bayan wannan kuma, akwai bukatun ruwan sha, kiwon lafiya, samar da dabbobi, batun makarantar miliyoyin yaran da suka kaura, musammun ma wadanda za su yi jarrabawa.

Bayan harin Boko Haram na baya bayan nan, da aka kai kan wani sansanin jami'an tsaro na FDS dake Bosson Nijar a ranar 3 ga watan Yuni, fiye da mutane dubu 50 ne suka tsere.

A yayin wata ganawa tare da kungiyoyin ba da tallafi da kudi dake taimakawa Nijar da kungiyoyin ba da agajin kasa da kasa a ranar Talata da yamma a birnin Niamey, faraministan Nijar Brigi Rafini ya kaddamar da wani kira ga kasashen abokan Nijar, da abokan hulda da kungiyoyin agaji domin su raka Nijar wajen daidaita matsalar gabashin kasar.

Tun cikin watan Febrairun shekarar 2015, yankunan gabashin Nijar, masu iyaka da Najeriya, musammun ma Bosso da Diffa, suke fama da hare haren Boko Haram, tun daga sansanoninsu na Najeriya, wadanda suka haddasa mutuwar daruruwan fararen hula da sojojin Nijar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China