in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da kungiyoyin gama kai 800,000 ne suka yi rajista a kasar Sin
2019-01-03 20:10:58 cri

Ministan kula da harkokin cikin gida na kasar Sin Huang Shuxian ya bayyana cewa, kasarsa ta yi rajistar sama da kungiyoyin gama kai 800,000.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin taron da aka watsa ta kafar bidiyo a yau Alhamis, ya ce, wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyoyin al'umma da na gidauniya da kungiyoyin masana'antu da kungiyoyi masu zaman kansu.

Bayanai na cewa, ma'aikatarsa ta gano irin wadannan kungiyoyi da suka sabawa doka kimanin 5,845 yayin aikin zakulo kungiyoyin da suka saba doka da ma'aikatar ta kaddamar a shekarar da ta gabata.

Ma'aikatar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi rajistar kimanin kungiyoyin aikin sa kai 12.000, baya ga masu aikin sa kai sama da miliyan 100 dake da rajista da suka yi aikin sa kai na sama da sa'o'i biliyan 1.2.

Ministan ya ce, a 'yan shekarun da suka gabata, ana samun karuwar yadda ake tafiyar da irin wadannan kungiyoyi da ma ayyukan sa kai a kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China