in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya yaba da nasarorin da Sin ta cimma karkashin manufar gyare gyare da bude kofa
2018-12-21 10:02:17 cri

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha a jiya Alhamis ya nuna yabo bisa ga nasarorin da kasar Sin ta cimma a cikin gwamman shekarun da suka gabata, inda ya bayyana manufar yin gyare gyare a gida da bude kofa ga waje ta kasar Sin da cewa manufa ce da ta dace.

"Mun gamsu da irin sauye sauyen da suka faru a kasar Sin. Na yi amanna ga kasa irin kasar Sin, wacce ke da yawan al'umma biliyan 1.3, zaman lafiya da hangen nesa suna da matukar muhimmanci, ciki har da batun tsara manufofi a cikin gida," Putin ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a taron manema labarai na shekara shekara.

Ya kara da cewa, "Zaman lafiya shi ne jigon da ya tabbatar da bunkasuwar kasar Sin," ya buga misali ne da manufar yin gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje ta kasar Sin.

Putin ya kuma yabawa dangantakar kut da kut dake tsakanin Sin da Rasha, kana ana sa ran adadin cinikayya dake tsakanin kasashen biyu zai kai dalar Amurka biliyan 100 a wannan shekarar.

Shugaban na Rasha ya nanata cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Rasha da Sin ya taimaka wajen kawo karin sauye sauye game da zaman lafiyar duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China