Gwamnatin kasar Sin ta yi Allah wadai da zargin da kasar Amurka ta yi mata game da batun tsaron intanet da kuma gurfanar da wasu Sinawa biyu bisa zarginsu da laifin satar bayanai ta intanet, kakakin ma'aikaar harkokin wajen kasar ne ta bayyana hakan a yau Juma'a.
Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta fitar, ta ce, zargin da Amurkar ta yi ba shi da tushe balle makama, zargin ya saba da muhimman ka'idojin kasa da kasa, kana zai iya lahanta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
"Kasar Sin ta yi fatali da wannan zargi, kana ta gabatarwa wakilan bangaren Amurka kurafinta kan wannan batu." in ji Hua.(Ahmad Fagam)