in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa dake ketare suna yabawa matuka kan jawabin da shugaba Xi ya yi a taron tunawa da cika shekaru 40 da aka aike "wasika ga 'yan uwa mazauna Taiwan"
2019-01-03 13:54:06 cri
A safiyar ranar 2 ga wata, an yi taron tunawa da cika shekaru 40 da aka aike "wasika ga 'yan uwa mazauna Taiwan" a babban dakin jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasa ta Sin. A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi.

Sinawa dake kasashen ketare sun nuna yabawa matuka kan jawabin da shugaba Xi ya gabatar, inda suka bayyana cewa, lardin Taiwan wani yankin kasar Sin ne da ba za a raba shi daga kasar ba, jawabin da shugaba Xi ya yi zai ba da babban gudummawa wajen raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.

Babban edita na jaridar Koran Baru Indonesia ta kasar Indonesia Li Zhuohui ya ce, jawabin da shugaba Xi ya yi ya nuna burinsa na ingiza ci gaban alakar gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan cikin kwanciyar hankali, ya kuma gabatar da dabaru masu amfani wajen warware wannan batu, lamarin da ya nuna girmamawa da fahimta ta shugaba Xi ga mutanen Taiwan.

A nasa bangare kuma, babban edita na jaridar Europe Times Online ta kasar Jamus Fan Xuan ya ce, bayanin da shugaba Xi ya yi, cewar "ya zama wajibi a tabbatar da kasancewar kasar Sin daya tak, kuma ko shakka babu za a cimma wannan burin" yana da karfi kwarai da gaske. Kuma wannan shi ne babban burin Sinawa dake kasashen ketare da kuma masu kishin kasa baki daya.

Shugaban kungiyar inganta zaman lafiya da wanzuwar kasar Sin daya tak ta kasar Tanzaniya Feng Zhenyu ya bayyana cewa, babbar manufar da shugaba Xi ya bayyana cikin jawabinsa ta nuna babbar moriyar jama'ar kasa, wadda za ta ci gaba da karfafa zaman lafiya da wanzuwar kasar Sin daya tak cikin lumana.

A nasa bangare kuma, shugaban kungiyar inganta zaman lafiya da wanzuwar kasar Sin daya tak ta kasar Masar Chen Jiannan ya ce, jawabin da shugaba Xi ya yi ya kara kwarin gwiwar Sinawa dake kasashen ketare, wadanda suke son bada gudummawar wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma wanzuwar kasar Sin daya tak.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China