in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jaddada adawarta ga shirin Amurka na sayarwa Taiwan makamai
2018-09-26 15:03:22 cri

Kasar Sin ta bayyana adawarta ga shirin Amurka na sayarwa Taiwan makamai bisa ko wani irin dalili.

An Fengshan kakakin ofishin dake kula harkokin lardin Taiwan na Majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce kasar ba ta amince da duk wani nau'i na tuntuba tsakanin jami'ai ko sojojin Taiwan da Amurka ba.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Amurka ta sanarwa majalisar dokokin kasar matakinta na sayar da makaman da darajarsu ta kai dala miliyan 330 ga Taiwan.

Ya kara da cewa, wadanda suke dagaro kan baki wajen gina kansu da kuma raina zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zirin Taiwan, za su gane kurensu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China