in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na kan turbar cimma muradunta a 2019, in ji shugaban kasar
2019-01-01 19:51:29 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kasar sa na kan turbar cimma muradun ci gaba da ta tsara a sabuwar shekarar nan ta 2019, aikin da a cewar sa ya zama wajibi a aiwatar da shi.

Cikin sakon sa na taya murnar shiga sabuwar shekara, shugaban ya ce burin gwamnatin sa shi ne ceto albarkatun kasar daga masu rub da ciki, dake fatan cimma burin kashin kai kadai.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, jam'iyyar sa ta APC mai mulki, ta yanke kudurin tunkarar gina kasa wadda za a yi amfani da albarkatun ta don inganta rayuwar 'yan kasa, ba tare da la'akari da banbancin siyasa ko bangaranci ba.

Ya ce gwamnati mai ci na fatan tabbatar da tsaro, da wanzar da zaman lafiya, da ci gaba, tare da bunkasa ababen more rayuwa, da baiwa kowa damar shiga a dama da shi a ci gaban kasa. Kaza lika yana fatan kafa kasa da kowa zai yi alfahari da ita, wadda za ta zama zakaran gwajin dafi tsakanin sauran kasashen duniya.

Daga nan sai ya sha alwashin jagorantar babban zaben kasar dake tafe bisa gaskiya da adalci, ta yadda kowa zai amince da sakamakon sa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China