in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun harbe mutane 14 a wani kauye dake jihar Kadunan Najeriya
2018-12-18 08:58:56 cri

Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane 14, tare da raunata wasu 17, yayin wani farmaki da suka kaddamar kan taron masu bikin aure a kauyen Paa-Gwandara dake karamar hukumar Jema'a a jihar Kadunan Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun kaddamar da harin ne da almurun ranar Lahadi, inda bayan yiwa taron jama'ar tsinke, suka bude wuta, kuma nan take suka hallaka mutane 9, yayin da wasu karin mutane 5 suka rasu a asibiti. Cikin wadanda suka jikkata dai har da yara kanana 6 wadanda a cewar wasu ganau suna ci gaba da samun kulawa jami'an lafiya.

Rundunar 'yan sandan yankin dai ta ce, ta fara gudanar da bincike game da aukuwar wannan lamari, kamar dai yadda shugaban karamar hukumar ta Jema'a Peter Averik ya tabbatar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China