in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya za ta inganta rayuwar masu bukata ta musammam
2018-12-04 09:48:37 cri

Ministar kula da harkokin mata da walwalar jama'a ta Nijeriya, Aisha Abubakar, ta ce gwamnatin kasar ta kuduri niyyar inganta rayuwar masu bukata ta musammam.

Aisha Abubakar ta bayyana haka ne jiya a Abuja, babban birnin kasar, yayin wani taron manema labarai da aka yi don ranar tunawa da masu bukata ta musammam ta duniya.

A cewarta, sai an karfafawa mutane gwiwa ne za su iya shiryawa cin gajiyar damarmakin dake akwai gare su, sannan kuma su zama mutane na kwarai tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a cikin al'umma.

Ministar ta shaidawa manema labarai cewa, karkashin manufar ma'aikatarta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, an aiwatar da shirye-shirye da dama dake da nufin kawar da kalubalen da masu bukata ta musammam suke fuskanta.

Ta kuma bayyana cewa, shirye shiryen da za a gudanar a ranar sun hada da rabon kayayyakin agaji da na'urorin da za su taimaka musu da ba su horo da shirye-shiryen karfafa gwiwa da kuma gwajin wadanda aka yankewa wata gaba ta jikinsu.

Har ila yau, ta ce an ware ranar ne da nufin wayar da kai don shawo kan kalubalen da masu bukata ta musammam ke fuskanta da samar musu da damarmaki da kuma sauya hallayar daidaikun mutane da manufofin gwamnati, ta yadda za su kyautatawa musu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China