in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya a shekarar 2018
2019-01-01 15:38:16 cri

Ko wace shekara kan zo da irin na ta yanayi, tattare da muhimman abubuwa dake shiga ran manazarta. Shekarar 2018 ba ta zama daban ba cikin shekaru masu cike da tarihi ga 'yan kasar. Najeriya ta gamu da na ta ababen faranta rai da kuma masu sosa rai.

A baya bayan nan, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya shaidawa wani taro cewa, a shekarar 2018, kasar ta sha fama da zub da jini sakamakon wasu tashe tashen hankula, a hannu guda kuma kasar ta yi nasarar fita daga yanayin matsin tattalin arziki, baya ga sauran kalubale daban daban. Shugaba Buhari ya ce shekarar 2018 na tattare da abubuwa masu faranta rai, da kuma akasan hakan.

A bangaren abubuwa masu faranta rai, Buhari ya ce Najeriya ta yi nasarar farfado da tattalin arziki, tun bayan fida daga matsayin da ta fuskanta na komadar sa. Ya ce, gwamnatin sa na aiwatar da manufar farafado da tattalin arziki da bunkasa shi yadda ya kamata. Masana da dama na ganin tattalin arzikin kasar na kan turba ta gari, duk kuwa tafiyar hawainiya a ci gaban sa.

Har wa yau fannin noma ya samu bunkasa, wanda hakan ya haifar da karin kudaden shiga ga kasar, karkashin sassan hada hadar cinikayyar ta da sauran fannoni na duniya.

Game da ababen more rayuwa kuwa, kasar ta yi nasarar rage gagarumin gibi a wannan fanni, inda ta samu manyan nasarori a fannin gina sabbin titunan mota, da layukan dogo, da kyautata filayen jiragen sama, da fannin samar da makamashi.

Bugu da kari Najeriya ta samu ci gaba a yakin da take yi da cin hanci da rashawa, yayin da kuma harkokin cinikayya ke kara inganta karkashin sauye sauye da mahukuntan kasar ke aiwatarwa.

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa ko EFCC, ta samu nasarar kammala shari'u da suka haura 300, tsakanin watannin Janairu da Disambar shekarar, adadin da ya haura na shekarar 2017 wanda bai wuce shari'u 189 ba.

A bangaren abubuwa marasa dadi kuwa, Najeriya ta sha fama da asarar rayukan al'ummarta, sakamakon kashe kashe na kabilanci, da wadanda ambaliyar ruwa ta haifar, da na gobara, da hadurran mota, da kuma na 'yan tada kayar baya.

Daga watan Janairu zuwa karshen shekarar ta 2018, alkaluma sun nuna cewa, mutane sama da 2,000 ne suka rasu sakamakon tashe tashen hankula daban daban, da suka auku a bangarorin kasar daban daban.

Kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, ta ci gaba da kaddamar da hare hare a sassan arewacin kasar, inda ta rika hallaka dakarun tsaro da fararen hula. A hannu guda kuma hare harenta sun raba miliyoyin mutane da matsugun nan su.

A cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar, sama da mutane 30,000 ne suka tsere wa gidajen su a shekarar, a jihohin da suka fi fama da wannan tashin hankali, wanda hakan ya dora matukar nauyi a wuyan sojoji da sauran jami'an tsaro, wadanda ya kamata a ce sun maida hankali kaco kan, ga aikin murkushe mayakan kungiyar ta Boko Haram, musamman ma a yankunan arewa maso gabashin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China