in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya bukaci a hada kai cikin sakon murnar sabuwar shekara
2018-12-30 16:03:49 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Asabar ya tabbatar da cewa, MDDr za ta ci gaba da hada kan al'ummar kasa da kasa domin gina wata muhimmiyar gada da kuma samar da kyakkyawan yanayi don lalibo bakin zaren magance manyan kalubalolin dake addabar duniya a shekarar 2019.

A sakonsa na taya murnar sabuwar shekara, babban jami'in MDDr ya ce, duniya tana fuskantar manyan matsaloli, a yayin da batun matsalar sauyin yanayi ke ci gaba da karuwa cikin sauri, ga kuma rarrabuwar kawuna dake kara kamari a sakamakon banbance banbancen siyasa, ga rashin daidaito dake ci gaba da ta'azzara, kana ga kuma yawan mutanen dake ci gaba da yin gararamba domin neman mafaka da kariya.

Duk da wadannan dunbun kalubaloli, Guterres ya ce, akwai kwarin gwiwar za'a iya samun mafita, ya yi karin haske game da irin nasarorin da aka samu a tattaunawa kan rikicin Yemen, da dinke barakar dake tsakanin Habasha da Eritrea, da rikicin Sudan ta kudu, da kuma batun aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris.

"A yayin da muke shirin shiga sabuwar shekara, ya kamata mu mayar da hankali wajen tunkarar kalubaloli, mu kare mutuncin bil adama da gina kyakkyawar makoma, ta hanyar yin aiki tare da juna," in ji babban sakataren.

"Idan kasa da kasa suka hada kai suka yi aiki tare, duniya za ta cimma nasara," in ji shi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China