in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankunan AIIB da NDB sun zama masu sa ido a zauren babban taron MDD
2018-12-21 11:11:37 cri

MDD ta amince da baiwa bankin raya ababen more rayuwa na nahiyar Asiya ko AIIB, da bankin NDB na kungiyar BRICS damar kasancewa 'yan kallo a ayyukan majalissar.

Zaman majalissar na jiya Alhamis ne ya amince da wasu kudurori guda biyu masu nasaba da hakan. Karkashin tanajin kudurorin, bankunan biyu za su samu damar kara shiga a dama da su, tare da ba da gudummawa wajen cimma ajandar ci gaba mai dorewa ta MDDr, kamar dai yadda wakilin dindindin na kasar Sin a majalissar Ma Zhaoxu ya tabbatar.

Mr. Ma ya kara da cewa, a matsayin Sin na hedkwatar wadannan bankuna biyu, kasar ta samu damar gabatar da kudurin gabatar da su ga majalissar, tare da ba da gudummawar samun amincewa da su.

Ya ce hakan ya shaida kwazon kasar Sin, game da goyon bayan cudanyar kasashen duniya daban daban, da fatan ta na yin hadin gwiwar aiwatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030.

A nasa tsokaci, babban jami'in zartaswa na bankin AIIB Gerard Sanders, ya ce bankin yana da burin yin hadin gwiwa, da sauran hukumomin dake da fatan samar da ci gaba a duniya, ta fuskar kirkirar tsare tsare, da aiwatar da manufofi da aka tsara.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China