in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a kasar Libya
2018-12-28 09:20:20 cri

Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta'addancin da aka kai ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar Libya, harin da ya hallaka mutane uku, wasu mutane 10 kuma suka jikkata.

Wata sanarwa da mambobin kwamitin sulhun suka fitar a jiya Alhamis, sun sake tabbatar da cewa, duk wani nau'i na ta'addanci na daga cikin manyan abubuwan dake kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

Sun kuma bukaci da a hanzarta zakulo wadanda ke da hannu, da wadanda suka shirya da masu daukar nauyin irin wadannan ayyuka na ta'addanci ta yadda za su girbi abin da suka shuka.

Mambobin kwamitin sulhun sun kuma bukaci kasashen duniya da su hada kai da gwamnati da hukumomin kasar ta Libya a wannan fanni.

Idan ba a manta ba, harin dai ya faru ne a ranar Talata da misali karfe 9 na safe agogon kasar ta Libya,lokacin da wata mota da aka dasa bam a cikinta ta yi bindiga a bayan ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Bayan aukuwar lamarin ne kuma, wani gungun masu dauke da makamai suka kutsa cikin ginin ta gaba da kuma bayansa, inda suka yi mummunan musayar wuta da dakarun tsaro.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China