Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kwamitin sulhun ya bayyana damuwa kan yadda aka gaza gudanar da zabuka a ranar 18 ga watan Nuwamba kamar yadda aka shirya. Ya kuma bayyana damuwa matuka game da shirye-shiryen gudanar da zabukan da aka shirya gudanarwa a ranar 10 ga watan Maris na shekarar 2019 dake tafe.
Sanarwar ta ce, shirya zabuka cikin adalci a 'yar karamar kasa dake yammacin Afirka a watan na Maris, zai share turbar wanzar da zaman lafiya a kasar.
Matakin farko na aiwatar da gyare-gyare a kasar, shi ne zabukan 'yan majalisun dokoki , gabanin zaben shugaban kasa da ake fatan shiryawa a shekarar 2019. (Ibrahim Yaya)