in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi kira ga bangarori daban daban na Guinee-Bissau da su warware rikicin siyasa ta hanyar tattaunawa
2016-05-28 12:54:07 cri
Jiya Jumma'a babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa ta yawun kakakinsa, inda ya nuna damuwa sosai kan zanga-zangar da aka yi game da nada sabon firaministan kasar Guinee-Bissau da shugaban kasar ya yi, ya kuma yi kira ga bangarori daban daban da su warware rikicin siyasa ta hanyar tattaunawa.

A cikin sanarwar Ban ya kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa na Guinee-Bissau da magoya bayansu da su dauki matakan da suka dace, don hana tsanantar rikici, kana da warware rikicin ta hanyar gudanar da tattaunawa.

Ban ya kuma cewa, rikicin siyasar da ake ta yi a kasar Guinee-Bissau ya kawo tasiri mai tsanani ga ayyukan hukumomin kasar, kana da kawo illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar. Saboda haka, Ban ya yi kira ga bangarori daban daban da rikicin ya shafa da su mai da hankali kan moriyar jama'ar kasar, tare kuma da daukar matakai bisa tsarin mulkin kasa, domin kawo karshen yanayi mai tsanani da ake ciki a kasar.

A ranar 26 ga wata, shugaba Jose Mario Vaz ya nada Baciro Dja firamimnistan kasar. Wannan ne karo na biyu da aka nada shi firaminista a cikin shekara guda. Saidai wannan nadin nasa bai samu amincewa daga wajen jam'iyyar da Baciro Dja yake ciki ba wato PAIGC. A sakamakon haka, magoya bayan jam'iyyar fiye dari sun taru a gaban fadar shugaba don nuna kin amincewarsu. A kafin haka dai, ba a cimma matsaya guda kan batun zaben firaministan ba a cikin jam'iyyar PAIGC.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China