in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya tsawaita wa'adin aikin dakarun wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
2018-03-01 12:32:12 cri
A jiya Laraba, kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin tsawaita wa'adin aikin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDDr a kasar Guinea-Bissau har na tsawon shekara guda, inda zai kare a ranar 28 ga watan Fabrairun 2019.

Kudurin dokar mai lamba 2404, ya bukaci MDD ta kara tsawaita wa'adin aikin jami'an kiyaye zaman lafiyar dake Guinea-Bissau (UNIOGBIS), domin su mayar da hankali wajen tallafawa yarjejeniyar da aka cimma ta Conakry, da kuma jadawalin yarjejeniyar da aka kulla na warware rikicin kasar ta hanyar hawa teburin sulhu don tattaunawar siyasa da kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Shirin na UNIOGBIS, ya kuma bukaci a kyautata tsarin mulkin demokaradiyya a kasar, musamman wajen gaggauta aiwatar da sauye-sauye a kasar. Haka zalika ya bukaci a taimakawa tsarin gudanar da zabe a kasar, don yin zaben mai cike da ingaci da kuma kafa ingantacciyar majalisar dokoki a kasar a shekarar nan ta 2018, bisa ga jadawalin zabukan da aka tsara tun da farko.

Ofishin ya kuma bukaci a samar da tallafi ga hukumomin kasar wajen ganin sun kammala aiwatar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Kudurin MDDr ya jaddada muhimmancin dake tattare da gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a bisa jadawalin da aka tsara wato a shekarar nan ta 2018, kana a gudanar da zaben shugaban kasar a shekarar 2019. Kasancewar majalisar na da muhimmanci matuka wajen amincewa da muhimman sauye sauyen da za su kawo kyautatuwar al'amurra a sha'anin zabukan kasar, da kuma samar da sabbin dokoki da suka shafi al'amurran jam'iyyun siyasar kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China