in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Libya ta ce ta shirya ba da tsaro yayin zabukan kasar
2018-10-15 10:00:08 cri

Rundunar sojin Libya dake da mazauni a gabashin kasar, ta ce a shirye take ta ba da tsaro ga duk wani zabe na kasar.

Wata sanarwa da ofishin yada labarai na rundunar ta fitar, ta tabbatar da cewa, rundunar ta damu da batun kare tsarin demokradiyya da kuma tabbatar da mika mulki lami lafiya.

Ta kuma bayyana shirinta na kare duk wani tsarin zabe a kasar ta hanyar ba da tsaro a rumfunan zabe a yankunan dake karkashin ikon sojoji.

A watan Mayun da ya gabata ne Faransa ta karbi bakuncin wani taro da ya hada bangarori daban-daban na Libya, da nufin kawo karshen takkadamar siyasar kasar.

Bangarorin sun amince su tabbatar da gudanar zabukan shugaban kasa da na majalisun dokoki da aka shirya yi ranar 10 ga watan Disamba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China