in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Italiya na karbar bakuncin taro kan Libya
2018-11-13 13:51:04 cri

An bude taron yini biyu kan Libya a birnin Palermo dake kudancin kasar Italiya jiya da yamma, da nufin samar da managartan matakan wanzar da zaman lafiya a kasar dake arewacin Afrika.

An tsaurara tsaro, inda aka girke 'yan sanda a kan titunan dake zagaye da wurin da ake gudanar da taron.

Firaministan Italiya Guiseppe Conte ya yi wa shugabannin tawagar dake halartar taron maraba. Dukkan bakin sun ci abincin dare tare a jiyan, bayan bikin bude taron da za a shafe yinin yau Talata baki daya ana yi.

Wata sanarwa da ofishin firaministan kasar ya fitar, ta ce Italiya ce ta shirya taron da hadin gwiwar shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Libya UNSMIL, domin samar da managartan shawarwari ga tsarin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Har ila yau, sanarwar ta ce taron na da nufin samar da ingantacciyar ci gaba a fannin tsaro da tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China