in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta sanya hannu kan aikin gina hanyar mota dala miliyan 305 da kamfanonin Sin 3
2018-10-25 10:22:49 cri

Hukumar kula da titunan mota ta kasar Habasha (ERA) a jiya Laraba ta sanya hannu don bayar da ayyukan gina titinan mota 5 a kan kudi kimanin dalar Amurka miliyan 305 wanda wasu kamfanonin kasar Sin uku za su gudanar da aikin.

Tsawon titunan ya kai kilomita 342.2, ana sa ran gina su ne a yankunan tsakiya, arewaci da kuma gabashin kasar.

Kamfamonin sun hada da kamfanin 21 na gina layin dogo na kasar Sin, da kamfanin CSCECL, da kuma kamfanin CCCC, wadanda za su gudanar da ayyukan gina hanyoyin biyar.

Da yake jawabi a lokacin bikin sanya hannu kan aikin a babban birnin kasar, darakta janar na hukumar ta ERA, Habtamu Tegegne ya ce, ayyukan gina titunan motar 5 za su taimaka wajen burikan da al'ummomin yankunan suka jima suna yinsa wanda kuma zai tabbatar da bunkasa tattalin arziki da yanayin zamantakewar al'ummar wadanda a baya suke fuskantar kunci a sanadiyyar rashin kyawun titunan mota.

Tegegne ya kara da cewa, aikin zai taimaka wajen saukaka zirga zirga, da kawo babbar moriya ga tattalin arzikin kasar ta Habasha baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China