Rahoton ya gabatar da cewa, tattalin arzikin teku na kasar Sin na samun saurin ci gaba, kuma an kara kyautatta tsarin masana'antu a fannin. Tun daga shekarar 2012, saurin karuwar tattalin arzikin kasar a kowace shekara ya fi bisa na karuwar tattalin arziki a lokacin guda. A shekarar 2017, jimillar kudi na tattalin arzikin teku ya kai RMB biliyan 7760, wadda ya kai 9.4% bisa na GDP.
A waje guda kuma, an samu kyautattuwar tsarin tattalin arzikin teku, kuma ana ta kara habaka hadin kai da kasashen duniya. Har ma aka samar da manyan yankunan tattalin arzikin guda uku masu halin musamman bisa tushen tattalin arziki, da yanayin da ake ciki, da kuma albarkatu. (Bilkisu)