Wannan gwaji dai ya alamta cewa, yanzu haka kasar Sin na da karfin gudanar da aikin ceto a cikin teku mai zurfin mita dubu uku ta hanyar amfani da wannan fasaha.
Za'a fara aiki da wannan na'ura ta mutum-mutumin mai na'ura ne nan ba da jimawa ba, yayin da hukumar kula da ayyukan ceto a teku ta birnin Yantai, ke ci gaba da samun babban ci gaba, a fannin inganta manyan tsare-tsaren da suka shafi harkokin teku na kasar Sin. (Murtala Zhang)