in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Tattalin arziki bangaren albarkatun ruwa ya fadada da kaso 7.5 bisa dari cikin shekaru 5
2018-01-22 10:29:04 cri

Awon tattalin arzikin kasar Sin mai nasaba da albarkatun ruwa ya samu ci gaba da kimanin kaso 7.5 bisa dari a tsakanin shekaru 5 da suka gabata, wanda yawan sa ya kai kaso 10 bisa dari na daukacin GDPn kasar baki daya.

Daraktan hukumar dake kula da albarkatun ruwa ta Sin ko SOA a takaice Wang Hong, ya ce a shekarar 2017 tattalin arzikin ruwa na kasar ya samar da kudi har yuan tiriliyan 7.8, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.22 a shekarar ta bara.

Mr. Wang Hong ya kara da cewa, cikin manyan ayyukan da SOA ta gabatar a baran, akwai tura masu sanya ido 11 zuwa yankunan dake makwaftaka da lardunan gabar ruwa, da manyan birane, da yankunan kasar domin tabbatar da ikon mallakar sassan ruwan kasar.

Kaza lika SOA ta gudanar da safiyon kasa baki daya, domin tabbatar da yanayin gurbatar ruwa, inda aka fayyace abubuwa dake gurbata ruwan har 9,600.

Har ila yau an samar da tsarin kula da ruwa a tsibiran Nansha, da tsarin fidda sakamakon hasashen yanayin muhalli a tuddan ruwa na Yongshu, da Meiji da Zhubi.

Jami'in ya ce, kasar Sin ta samu sakamako mai gamsarwa a fannin binciken sassan ruwa, ciki hadda wanda jirgin ruwan Xuelong dake fasa kankara da jirgin nutso a teku na Jiaolong suka gudanar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China