in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta hukunta jami'ai sama da 10,000 bisa saba dokar aiki a Nuwamba
2018-12-25 09:38:27 cri

Babbar hukumar dake yaki da rashawa ta kasar Sin ta sanar da cewa, kimanin mambobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jami'an gwamnatin kasar 10,295 ne aka zartarwa hukunci bayan samun su da hannu wajen saba dokar aiki a cikin watan Nuwamba.

An samu jami'an ne da hannu dumu dumu wajen aikata laifuka kimanin 7,249, in ji sanarwar, wadda kwamitin tsakiya na hukumar tabbatar da da'a da bin diddigi na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) ta wallafa a shafinta na intanet.

Fitar da kudaden alawus ko kuma kudaden kari ba bisa ka'ida ba, na daya daga cikin irin laifuka da aka fi yawan aikatawa, sai kuma bayar da cin hanci ko kuma karbar rashawa da kuma yin amfani da kudaden gwamnati wajen shirya bukukuwa ko taruka ba bisa ka'ida ba.

Kimanin jami'ai 78,804 ne aka samu da hannu wajen aikata laifuka 55,705, wadanda tuni aka hukunta su a watanni 11 na farkon shekarar 2018, in ji sanarwar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China