in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karancin kudade na haifar da tsaike ga yaki da cin hanci a Afirka
2018-11-29 10:24:08 cri

Mai shigar da kara na kasar Afirka ta kudu, kana mataimakin shugaban kungiyar masu rajin kare hakkin dan Adam da shiga tsakani ta Afirka (AOMA) Busisiwe Mkhwebane ya bayyana cewa, karancin kudade na kawo tarnaki ga matakan nahiyar Afirka na yaki da cin hanci.

Busisiwe ya ce, galibin hukumomin dake rajin kare hakkin dan-Adam ba su da isassun kudaden da za su iya shiga yankunan karkara don sauraron korafe-korafen dake da nasaba da cin hanci.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayin bude babban taron zauren MDD karo 6 kan kungiyar ta AOMA.

Shi ma ministan shari'a, kana babban lauyan gwamnatin Rwanda Johnson Busingye ya bayyana cewa, taken taron ya dace da kudirin kungiyar tarayyar Afirka na yaki da cin hanci a matsayin hanyar farfadowar nahiyar.

Taron wanda za a kammala a gobe Jumma'a, ya hallara wakilai daga kasashen Afirka sama da 40, bisa taken "Rawar da masu rajin kare hakkin dan-Adam da shiga tsakani ke takawa wajen yayata gaskiya da shugabanci na gari a Afirka". (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China