in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da bayanan 'yan kasarta da suka tsere kasashen waje
2018-06-07 10:28:34 cri

A jiya Laraba gwamnatin kasar Sin ta fitar da bayanan wasu 'yan kasar su 50 wadanda ake zarginsu da hannu wajen aikata laifukan dake da nasaba da yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa, bayanan ya kunshi sunaye da hotunansu, har ma da wuraren da ake kyautata zaton suna zaune a halin yanzu.

Bayanan dai sun hada da jinsi, da katin shedar dan kasa, da lambobin fasfo, matsayinsu na aiki a baya, da ranar da suka tsere daga kasar ta Sin, har ma da irin laifukan da ake tuhumarsu da shi, kamar yadda ofishin dake kula da maido da 'yan kasar da suka tsere da maido da dukiyar gwamnati da aka wawashe karkashin kwamitin tsakiya mai kula da yaki da rashawa ya sanar.

Mafi yawan wadanda suka tsere din, ana zarginsu ne da aikata laifukan rashawa, cin hanci, ko kuma barnata dukiyar gwamnati. Daga cikin mutanen 50, 21 daga cikinsu sun tsere daga kasar ne sama da shekaru 10 da suka gabata.

Ofishin wanda ke bukatar taimakon jama'a, ya kuma bude wani shafi ta intanet, inda zai dinga karbar bayanai game da Sinawan da suka tsere daga kasar, kuma ya ba da tabbacin ba da kariya ga duk wanda ya fallasa mutanen da ake zargin.

Shirin na kasar Sin na "Sky Net" ya samu nasarar tattara bayanan Sinawa kimanin 4,141 wadanda suka tsere zuwa kasashe da yankunan duniya sama da 90, kuma ya samu nasarar kwato kudade da yawansu ya kai yuan biliyan 10 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.56 ya zuwa karshen watan Afrilu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China