in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta yi Allah wadai da harin bom da aka kai kasar Somalia
2018-12-24 11:03:24 cri
Kungiyar neman samun cigaba tsakanin gwamnatoci ta gabashin Afirka IGAD ta bada sanarwa a jiya Lahadi, inda ta yi Allah wadai da wani harin bom da kungiyar ta'addanci ta al-Shabab ta kaddamar kan wata tashar binciken motoci da sojojin kasar Somalia suka kafa a Mogadishu, fadar mulkin kasar, a ranar Asabar da ta gabata.

Sanarwar ta IGAD ta jiyo babban sakataren zartaswar kungiyar IGAD, Mahboub Maalim, yana cewa, "Muna goyon bayan jama'ar kasar Somalia da gwamnatin kasar wajen yin Allah wadai da wannan mummunan aiki na ta'addanci da aka aikata, kana muna jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayuka sakamakon harin, tare da fatan wadanda suka jikkata za su warke cikin sauri. "(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China