in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Ana aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya bisa bukatun kasuwa da kasuwanci
2018-11-19 19:10:08 cri

Yau Litinin a nan birnin Beijing kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, ana kokarin ciyar da shawarar ziri daya da hanya daya gaba da gwamnatin kasar Sin ta gabatar bisa bukatun kasuwa da kasuwanci karkashin akidar martabar juna da samun moriyar juna.

Rahotanni na cewa, kwanan baya mataimakin shugaban kasar Amurka Michael Pence ya gabatar da wani jawabi yayin taron shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu na kungiyar APEC, inda ya bayyana cewa, kasarsa za ta samar da taimakon kudi dala biliyan 60 ga kasashen dake yankin tekun Indiya da tekun Pasifik domin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, ba tare da gindaya wani sharadi ba. Wasu kafofin watsa labarai suna ganin cewa, dalilin da ya sa Pence ya fadi haka shi ne domin zargin kasar Sin, kan wannan, Geng Shuang ya jaddada cewa, idan kasar Sin ta gindaya sharadi, to ba zai yiyu ba a kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da yawan gaske, idan kasar Sin ta samu moriya daga shawarar kawai, to ba zai yiyu ba kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 140 bisa shawarar ziri daya da hanya daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China