in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana fatan kasashen duniya za su kara karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka
2018-12-14 19:05:27 cri

Yau Juma'a kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, har kullum kasar Sin tana goyon bayan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da ma sauran kasashen duniya, tana kuma maraba da al'ummomin kasashen duniya da su kara zuba jari a kasashen Afirka bisa tushen martabar su domin ciyar da kasashen Afirka gaba yadda ya kamata.

Kwanan baya mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa John Robert Bolton ya gabatar da wani jawabi, inda ya sanar da sabuwar manufar da gwamnatin Trump za ta aiwatar kan kasashen Afirka, kuma ya zargi kasashen Sin da Rasha wai suna kwace dukiyoyi a nahiyar Afirka, har suna kawo barazana ga tsaron kasar ta Amurka, kana ya jaddada cewa, makasudin fitar da sabuwar manufar shi ne domin dakile tasirin da kasar Sin take da shi a kasashen Afirka.

Kan batun, Lu Kang ya yi nuni da cewa, Amurka ta fitar da manufa ce ba domin kasashen Afirka ba, sai dai domin Sin da Rasha, a fili ta ke cewa, za a san wanda ke kawo alheri ga al'ummun kasashen Afirka, da kuma wanda ke kwace dukiyoyin kasashen Afirka.

Jami'in ya kara da cewa, tarin shugabannin kasashen Afirka sun taba bayyana cewa, kasar Sin tana samar da taimako da goyon baya ga kasashensu ne ba tare da gindaya kowane sharadin siyasa ba, kana kasar Sin ba ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashensu, har ma sun yaba wa kasar Sin cewa, kasar Sin sahihiyar aminiyar kasashen Afirka ce wadda ke samar da taimako yayin da suke kokarin farfado da kasashensu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China