in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: WTO ba Amurka ce ta kafa ta ba
2018-11-22 20:34:27 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, wasu Amurkawa sun bayana a asirce cewa, za a kori kasar Sin daga kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, hakan ya nuna cewa, Amurka tana nuna fin karfi, kasar Sin tana nacewa ga manufar yin harkokin cinikayya tsakanin bangarori da dama a karkashin jagorancin WTO, tana son hada kai da sassa daban daban domin ganin an yiwa ayyukan kungiyar gyaran fuska.

Jami'in ya jaddada cewa, tun bayan da kasar Sin ta shiga WTO, ta samu yabo daga wajen sassa daban daban, har kullum kasar Sin tana nacewa ga manufar gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, tare kuma da kiyaye martabar tsarin duniya bisa tushen ka'idojin da aka tanada, kana tana fatan hada kai tare da sauran kasashen duniya domin kafa sabuwar hulda tsakanin kasa da kasa mai martaba da juna da adalci da kuma moriyar juna, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar bil Adama kamar yadda ake fata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China