Kungiyar Paradise Foundation International PFI, dake da mazauni a kasar Sin, ta ce tana shirin karrama 'yan Afrika 50 da suka yi fice wajen kare hallitu da muhallin dawa.
Kungiyar PFI da kungiyar kare namun daji ta gabashin Afrika da kuma asusun Mara Conservation, sun wallafa wata sanarwa a jaridar Star daily, inda suke bukatar a mika musu sunayen wadanda suka cancanci karamawar, wadda ita ce irinta ta farko da kungiyar za ta yi.
Wadanda za su ci gajiyar kyautar dala 3,000 sun hada da masu kare namun daji da dazuka da sauran jami'an dake gaba-gaba wajen kare namun daji da muhallin hallitu da kuma albarkatun kasa.(Fa'iza Mustapha)