in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Sin na iya tallafawa Afirka a fannin raya yankin ciniki cikin 'yanci
2018-05-24 09:37:00 cri

Daraktan sashen bunkasa kwarewar ayyuka a hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD ko UNECA a takaice, Mr. Stephen Karingi, ya ce kasar Sin na iya tallafawa kasashen nahiyar Afirka, da dabarun cin gajiyar tsarin su na samar da yankin ciniki cikin 'yanci.

Stephen Karingi, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar sa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin kasar Kenya. Ya ce, idan har nahiyar Afirka na son cin cikakkiyar gajiya daga tsarin cinikayya cikin 'yanci, to ya zama wajibi kasashen ta su mai da hankali kan raya sabbin sassan zuba jari, da na samar da ababen more rayuwa, da na samar da kwarewar ayyuka da kere kere.

Jami'in ya ce, da yake Sin na da kwarewa a dukkanin wadannan sassa, tana iya agazawa Afirka, ta yadda ita ma za ta kai ga amfana daga fasahohin raya yankin ta na cinikayya cikin 'yanci.

Mr. Karingi ya yi tsokacin ne, a gefen taron karawa juna sani da aka shirya na kwararru, game da bunkasa samar da ababen more rayuwar jama'a, taron da aka yiwa lakabi da PICI.

Jami'in ya kara da cewa, akwai bangarori da dama da Sin za ta iya yin hadin gwiwa da Afirka, wajen sassauta yanayin cinikayya ta kan iyakokin nahiyar. Ya ce, kasar Sin ta dade tana tallafawa Afirka, amma har yanzu akwai sauran sassa da nahiyar za ta iya amfana daga gare su, musamman ma fannin inganta sha'anin sufurin jiragen sama, wanda Sin din ke da kwarewa a kan sa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China