in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Gyare-gyare da bude kofa# Kasar Sin ta kira taro don murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida
2018-12-18 10:46:33 cri

A safiyar yau Talata ranar 18 ga wata, aka kira babban taro a birnin Beijing, don murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, inda babban daraktan kwamitin tsakiya na Jam'iyya Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kwamitin soja na kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron da kuma ba da jawabi.

A ranar 18 ga watan Disamban shekarar 1978, an kira taro na uku na dukkan wakilan kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar, inda aka tsai da kudurin mai da hankali kan raya tattalin arziki, da aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida.

A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu sauyi daga tushe a dukkan fannoni. Inda matsakaicin jimillar GDP ya karu da 9.5% a ko wace shekara, yayin da matsakaicin kudin shiga da jama'a ke iya amfani da su ya ninka sau 22.8, baya ga yadda yawan masu fama da talauci da ya ragu da miliyan 740, har ma yawan gudummawar da kasar Sin ta ba duniya ta fuskar tattalin arziki ya zarce 30% a jerin shekaru da dama.

Bugu da kari, a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta bude kofarta ga waje don raya kanta, lamarin da ya sa jimillar cinikayyar shige da fice ta hajoji ta ninka har sau 198, yayin da jimillar cinikayyar shige da fice ta aikin ba da hidima ta ninka fiye da sau 147. Kaza lika yawan kudin waje da Sin ta jawo kuwa ya zarce dala biliyan 2000 gaba daya.

Ya zuwa yanzu dai, kasar Sin ta riga ta zama kasa mafi girma ta biyu a duniya ta fuskar tattalin arziki, da kasa mafi girma ta farko ta fuskar masana'antu, kuma mafi girma ta farko ta fuskar cinikayyar hajoji, kuma mafi girma ta farko ta fuskar kudaden ajiyar ketare a duk duniya. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China