in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin: Ya kamata a goyi bayan kasashen tsakiyar Afirka bisa tushen martaba ikon mulkinsu
2018-12-15 15:30:08 cri

A kwanan baya ne zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana cewa, yayin da kasashen duniya suke nuna goyon bayansu ga kasashen dake yankin tsakiyar Afirka, a fannin dakile barazanar da suke fuskanta, kamata ya yi su rika martaba ikon mulkin kasashen, haka kuma su tabbatar da ci gaban tattalin arzikin yankin bisa tushen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Yayin da ake bincike game da batun yanayin da kasashen dake yankin tsakiyar Afirka ke ciki, da rundunar sojoji ta Lord's Resistance Army, jami'in na kasar Sin ya bayyana cewa, ya dace kasashen duniya su kara mai da hankali kan batutuwan, haka kuma su kara nuna goyon baya gare su.

Jami'in ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yaba da kokarin da MDD ke yi, kana kamata ya yi kasashen duniya su kara samar da taimako ga kasashen dake yankin tsakiyar Afirka, wajen yaki da fataucin makamai, da miyagun kwayoyi tsakanin kasa da kasa, da kuma dakile ayyukan ta'addanci, da manyan laifuffuka na kungiyoyin bata gari, ta yadda za a gaggauta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Wu Haitao ya kara da cewa, kasar Sin tana son kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen tsakiyar Afirka, kuma za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan hukumomin MDD a yankin, tare kuma da taka rawa a fannin kiyaye zaman lafiya, da dakile matsalar tattalin arziki, da ayyukan jin kai a yankin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China