in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya yi kira da a dauki kwararan matakan ceto tattalin arzikin Afirka daga durkushewa
2016-05-04 09:42:09 cri

Asusun ba da lamuni na duniya IMF a takaice ya yi kira da a dauki kwararan matakai don shawo kan matsalolin da ke haddasa karuwar koma bayan tattalin arzikin nahiyar Afirka.

Asusun na IMF ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da rahoto game da hasashen tattalin arzikin kasashen nahiyar da ke yankin kudu da hadamar Sahara na shekara ta 2016, yana mai gargadin cewa, ana hasashen tattalin arzikin nahiyar zai yi kasa da kaso 3 cikin 100 a shekarar 2016, wato koma bayan da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 15.

Bayanai na nuna cewa, ko da a shekarar da ta gabata, ci gaban tattalin arzikin nahiyar kashi 3.5 cikin 100 ne kawai. Yayin da a cikin shekaru goma da suka gabata, ci gaban ya kai kusan kaso 6 cikin 100.

Masana na alakanta wannan koma baya kan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da ya shafi galibin kasashen na Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara, kamar su Najeriya, Angola da kasashe kamar su Ghana da Afirka ta Kudu da Zambia da su ma faduwar farashin man ya shafi bangaren da ba na makamashi ba da ake fitarwa zuwa ketare.

Baya ga wadannan matsaloli, ita ma matsalar fari da ta gallabi galibin kasashen da ke gabashin Afirka tana cusa miliyoyin jama'a cikin barazanar matsalar karancin abinci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China