in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta bukaci a aiwatar da hadakar matakai domin dakile kaurar jama'a ba bisa ka'ida ba
2018-12-18 09:22:58 cri

Wani jami'in hukumar kwatam a Algeria, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki game da yakin da ake yi da kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba, da su yi amfani da dabarun gwama ayyukan jin kai da na kyautata tsaro, muddin ana fatan shawo kan matsalar kaurar jama'a ta barauniyar hanya.

Daraktan sashen ayyukan da suka shafi kaurar jama'a a ma'aikatar cikin gidan kasar Algeria Hassan Kacimi ne ya bayyana hakan, yayin da yake tsokaci ta kafar radiyon Channel III dake kasar.

Kacimi ya ce, kasar sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen kare iyakokin ta daga bakin haure dake yunkurin tsallakawa kasar ba tare da bin tanajin doka ba. Jami'in ya ce, Algeria na fuskantar babbar barazana ta kwararar bakin haure daga kasashen yankin kudu da hamadar Saharar Afirka.

Ya ce, akidu irin na masu tsattsauran ra'ayi, na yin tasiri ga kwararar bakin haure, don haka aikin kare kan iyakokin kasar da rundunar sojin kasar ke yi na da ma'anar gaske.

A baya bayan nan dai mahukuntan Algeria sun mayar da bakin haure da dama da suka shiga kasar ta barauniyar hanya gida. To sai dai kuma a watan da ya gabata, mai magana da yawun ofishin kare hakkokin bil Adama na MDD Ravina Shamdasani, ta yi kira ga mahukuntan kasar ta Algeria, da su dakatar da mayar da bakin haure gida, tana mai cewa, hakan na iya ruwa wutar wariyar launin fata, da kin jinin wani jinsi tsakanin al'ummun yankin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China