in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta yi watsi da gina cibiyar tsugunar da bakin haure marasa rajista
2018-07-16 09:59:22 cri

Gwamnatin Algeria ta sanar a jiya Lahadi cewa, ana kokarin shafa mata kashin kaji game da manufofin kasar dangane da bakin haure, inda kasar ta nanata aniyarta ta yin watsi da batun gina cibiyar tsugunar da bakin haure marasa rajista a cikin kasarta.

Ministan cikin gidan kasar Algeria Nouredine Bedoui ne ya bayyana hakan a lokacin bude taron kwamitin hadin gwiwar kasashen Algerian da Nijer karo na 6, a babban birnin kasar Algiers.

Bedoui ya ce, a ko da yaushe kasarsa tana kokarin dakile kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba, kuma a ko da yaushe tana taimakawa bakin hauren na kasashen Afrika, kuma ba ta taba yin kasa a gwiwa ba a kokarin taimaka musu da kayan tallafin jin kai wanda ya kai ma'auni na kasa da kasa.

Ya kara da cewa, kasar Algeria ta yi watsi da batun kafa wani yankin musamman na tsugunar da bakin haure ba bisa ka'ida ba a cikin kasarta.

Bedoui yana mayar da martani ne game da sukar da wasu kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin dan adam ke yi game da matakin da kasar ta dauka na yanke shawarar tisa keyar dubban 'yan ci rani daga Afrika zuwa kasashensu na asali, bayan da aka bukaci kasar ta arewacin Afrika ta gina cibiyoyi na muasamman na tsugunar da bakin hauren marasa rajista.

Bedoui ya bukaci a kara hadin gwiwa mai karfi tsakanin kasar Algeria da jamhuriyar Nijer don shawo kan matsalar kwarar bakin hauren, ta hanyar yaki da bata gari da masu safarar bil adama, da kuma dakile tashin hankali na masu tsattsauran ra'ayi.(Ahmad FAgam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China