in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan saman Najeriya sun yi ruwa wuta a kan maboyar Boko Haram
2018-11-27 09:05:59 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mayakan saman kasar sun yi luguden wutan a kan maboyar mayakan Boko Haram, bayan wani mummunan harin makon da ya gabata da mayakan na Boko Haram suka kai a kan wani sansanin sojojin kasar dake yankin Metele a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, harin da ya hallaka sama da sojojin kasar 70.

A cewar kafar watsa labarai ta PR Nigeria dake Abuja, fadar mulkin Najeriya, harin na baya-bayan nan da mayakan saman kasar suka kai, ya lalata kwanban motocin da mayakan Boko Haram suka yi amfani da su wajen kaiwa sansanin sojojin Najeriyar dake yankin Metele hari.

Majiyar ta ce, rundunar sojojin saman Najeriyar ta yi amfani da jirage masu saukar ungulu na zamani sanfurin Mi-35M wajen lalata sansanonin mayakan na Boko Haram.

A jawabin da ya gabatar bayan samun labarin kaiwa sojojin kasar hari, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana kaduwa matuka da kisan sojojin, yana mai bayyana kudurin gwamnatinsa na samarwa sojojin da ma daukin al'ummar kasar cikakken tsaro.

Bugu da kari, shugaba Buhari ya tura ministan tsaro Mansur Dan-Ali zuwa kasar Chadi don yin ganawar gaggawa da shugaba Idriss Deby na kasar Chadi, game da tabarbacewar tsaro a kan iyakar kasashen biyu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China